Thursday 27 July 2017

'YAN NAGERIA A HALIN KUNCI



'YAN NAJERIYA  A HALIN MATSIN RAYUWA;
INA MAFITA?
DAGA
MUDASSIR ALIYU YUNUSA
mudassiray@gmail.com

A bayyane lamarin yake game da irin dunbin arzikin da Allah ya huwacewa Najeriya ta fuskoki da dama, ta inda kowanne yankin siyasa na kasar ke tunkaho da wani abun arziki da ka iya basu damar cigabansu dungurungum ba tare da hankoro ba. Misali arewacin Najeriya wanda ke da fadi da albarkar kasa suna alfahari da noma, kiwo da sana'o'i daban daban, anyi ittifakin arewa kadai idan aka inganta harkar noma ya dace da na zamani zata iya nomawa daukacin nahiyar afirka abinci na tsawon shekara daya, banda kuma sauran ma'adanai masu daraja irinsu kuza, zinare kai harma da tunkuzar danyen man fetur. Haka abin yake a bangaren yammaci da gabashin kasar. Sai dai abin takaicin shine yadda hukumomin kasar kama daga gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomin sukai watsi da irin tagomashin arzikin da ke kasar suka maida hankali kacokan akan danyen man fetur da ake hakowa a kudancin kasar. Ba komai yaja hankalin gwamnati ba illa irin dinbin kudaden shiga da kasar ke samu wajen kasuwancin mai, kodayake tabbas an samu alfanu matuka a lokacin da kasuwar danyen man ke damawa a duniya, sai dai kash! A halin yanzu farashin danyen man ya fadi warwas lamarin da ya jawowa Najeriya jangwamgwama ta fuskar tattalin arziki wanda ya haifar da matsalolin rayuwar da ke addabar jama'ar kasar musamman marasa karfi.
Tun farkon shekarar 2015 abubuwa ke tabarbarewa musamman yadda hankalin shugabannin kasar ya karkata akan babban zabe wanda jama'a ke dar dar da zuwansa, abun da ya jawo koma baya a harkar sanya hannun jari a cikin gida. Abubuwa sun sake tabarbarewa bayan faduwar gwamnati mai mulki musamman  a lokacin da ake shirin mika mulki ga zababbiyar gwamnati lamarin da ya sa kasar ta kama hanyar durkushewa musamman a satin karshe na mulkin PDP. Bayan rantsuwa jama'a kasar nan sun saka ido don ganin irin salon mulki na sabuwar gwamnati hade da sauraron chanjin  da aka alkawaranta musu, duk da yake ba zai yiwu ace an sami chanji kamar yadda jama'a ke tunani ba saboda irin lalacewar al'amura tsawon lokaci amma duk da haka tabbas Najeriya da mutanenta suna cikin halin NI 'YASU.  An sami jinkiri wajen nada ministoci lamarin da ya sa ake ganin da zaran an nada su to za'a fara samun sassauci ko kadan ne, sai dai duba da irin matsalolin da talakawa ke fuskanta ya janyo cecekuce. Babbar matsalar da talakawa suka fara fuskanta itace yadda wahalar man fetur tai kamari a karshen shekarar bara da kuma watannin  farkon  a bana, har ta kai farashin lita ya nunka sau biyu kuma duk da tsadar ma da kyar ake samu a gidajen mai sai a kasuwar dare wanda lita daya ake sayenta N300 galan kuma N1200, wannan lamarin yana matukar ciwa jama'a tuwo a kwarya, na biyu kuma yadda darajar Dalar Amurka ke hauhawa Naira kuma take cigaba da faduwa musamman ganin yadda dalar ta zamo babban sinadarin tafiyar da Kasuwanci a cikin gida da wajen kasar. Haka kuma rufe iyakoki da hana shigo da wasu kayan abinci dana masarufi cikin kasar ba tare da wani shiri ko tanadi mai kyau ba shima ya sake rikirkita jindadi da walwalar yan Najeriya, Kwatsam kuma sai ga rahoton hukumar kididdiga ta kasa da ya nuna karara fadawar Najeriya cikin yanayin Tabarbarewar tattalin arziki, lamarin da ya kara dagula halin rayuwar al'umma duba da yadda Farashin kaya ya kara hauhawa ninkin baninki ta yadda talakawa wadanda suka fi yawa a kasar ke dandana kudarsu. Matsalar karancin aikinyi ta addabi matasa wanda a kullum ke jefa su cikin mayuyacin hali da mugun tunani. Tabarbarewar tafiyar da ayyukan gwamnati ga jama'a da kuma  koma bayan da jama'a ke fuskanta wajen saukin rayuwa wanda karuwar talauci da rashin madogara suka haifar a wannan lokacin na daga cikin abubuwan da suke yawo a cikin zukatan wasu yan Najeriya musamman dangane da lamarin gwamnati mai ci yanzu, ga kuma rashin sanin hakikanin nasarar da kasafin kudin bana (2016 Budget) ya samu duk da irin tataburzar da aka sha kafin a tabbatar dashi Wanda ya kawo kusan tsakiyar shekara ba a gabatar da shi ba.
To ina mafita? Shawara ta ga gwamnati duk da yake akwai matsalolin da suka gada daga gwamnatin da ta shude  kima ya kamata gwamnatocin da suka gabata ace sun tsarawa kasarnan sahihiyar hanyar cigaba musamman a lokutan da kudi ba matsala bane inda za'a saka kudin ne aka saka ba dai dai ba, wasu kudaden sun shige lalitar wasu tsirarun jama'a da suka sami damar  sahalewar amanar yan kasa
 Duk da haka gwamnati a halin yanzu ya kamata tai wani abu cikin gaggawa don magance matsalolin musamman matsalar bakin talauci da tsananin wahalar rayuwa wanda akasari tsadar kayan abinci da na masarufi ya jawo ganin yadda jamaa ke fama da harkokin yau da kullum na jama'ar Najeriya, ina da yakinin cewar gwamnati tana sane da halin da yan kasa ke ciki don sau da yawa takan fito ta bayyana hakan gami da bada hakuri sai dai tabbas akwai bukatar hankalin gwamnati a aikace don magance wannan matsalar.
A karshe ina son shaidawa gwamnatin Najeriya cewar yanzu fa lokaci yayi da ya kamata su fadada hanyoyin samun kudin shiga musamman duba da irin yadda darajar danyen man da kasar ke tinkaho dashi ke cigaba da faduwa warwas a kasuwar duniya. Ya zama tilas a san abun yi don gudun fadawa babban kalubalen matsanancin tattalin arziki wanda yafi na yanzu (Allah ya kiyaye) wanda ka iya zama babban chikas wajen samarwa 'yan kasa kayan more rayuwa kamar yadda aka alkawaranta musu lokacin kamfe.

MUDASSIR ya rubuto daga NTA Zariya

No comments:

Post a Comment