TUR! DA MUJALLAR
CHARLIE HEBDO
DAGA
MUDASSIR ALIYU
YUNUSA
NTA ZARIYA
mudassiray@gmail.com
Addini shi ne hanyar rayuwa
bisa bautar wani abun bautawa,
ta hanyar amfani da tsare-tsaren da
wannan abin bautar ko kuma
makusantansa suka tanadar
domin tafi da rayuwar yau da
kullum bisa wasu tanaje-tanaje
ko tsare-tsare. Addini ya rabu
gida daban-daban, kamar yadda
masana addini su ka yi bincike
kuma su ka tabbatar, wanda a tsarin bauta
kowa nada 'yancin yin addininsa ba tare da cin zarafi ba, kuma a ka'ida bai kyautuwa
ga mabiya addinai cin dunduniya ko aibata wani ko wasu ginshikai na wani addinin
daban. Misali, addinin musulunci wanda ya bukaci bawa ya mika wuya kacokan ga
Allah ubangijin Halittu, da kuma yin imani da manzon Allah Annabi Muhammad (Tsira
da aminci su tabbata a gareshi) da kuma kafatanin annabawa da manzannin Allah.
Haka kuma musulunci ya haramta zalinci akan kowa ba kadai sai iya mabiya addinin
ba, baya halatta ga musulmi na kwarai ya cutar da wani ko wasu al'ummar da basa
bin addinin ballantana kuma mabiya addinin bai daya, yin hakan ka iya jawo fushin
ubangijin saboda irin zaman lafiya da masalahar da ke cike a cikin addinin na musulunci.
Hakazalika a addinin kiristanci dana yahudanci, tanade tanaden addinan tun asali
basu bada damar suka ko cusgunawa wasu mabiya addinan da suka sha bamban da nasu
ba.
Zance na gaskiya addinin musulunci ya koyar da yin da'a,
biyayya da kuma yarda da dukkan annabawa da mursalan da Allah (SWT) ya aiko su tun
daga Annabi Adam (AS) har zuwa cikamakonsu kuma jagoransu Annabi Muhammad (SAW),
wanda rashin yin imani dasu ka iya
ruguza musukuncin dan adam.
Tun a shekarun baya a yankin turai ake samun wasu tsagerun
mutane da suka himmatu wajen cin zarafin musulmai ta hanyar rubutu ko zanen mutum
mutumin don yin izgili gaAnnabin Allah don dai kawai a kuntatawa musulunci da musulmai
wai suna Ikirarin 'yanci ne na magana ko kuma 'yancin yan jarida ya bada wannan
damar. Ai wayewa ba hauka bace, kuma wannan lamarin duniya ta san cewar ana aiwatar
dashi ne don a turawa mabiya addinin musulunci haushi duk da suna batun 'yanci
to ai harda 'yancin gudanar da addini ga jama'a a fadin duniya. Duk da sanin
rashin dacewar abin amma jagoranci duniya bai daukar wani kwakkwaran mataki ganin
yadda abin ke ta da hankulan mabiya addinin na musulunci. To wai me ake nufi da
musulmin duniya? Na farko dai ina dalilin yin wannan batancin? Shin takalar fada
akeyi ko kuwa so ake a nunawa duniya musulunci ba a bakin komai yake ba?
Kamar yadda na fada a farko babu addinin da ya aminta
aci zarafin wasu masu bautar daban, to in
haka ne me zai sa shuwagabannin irin wadannan sakarkarun mutanen baza su ja musu
kunne ba su kuma nuna rashin a mincewarsu karara. Ni kam nayi imanin musulmin kwarai
ba zai taba munzata wani ko wasu don kawai suna da banbancin addini, kai koda kuwa
hakan ta faru to zakaji malaman muslunci sun fito sun soki abin. Kodayake Kalilan
daga mabiya addinin kiristanci sun yi tur da ayyukan batancin, sai dai tun a
shekarun baya da hakan ta faru a kasar Denmark har ila yau abun kara bayyana yake
kuma wannan shine dalilin da ya tunzura wasu matasa daukar hukuncin da hannunsu.
Duk da yake daukar hukunci ko doka ahannu ya saba da ka'idar musulunci amma bai
kamata a bar dukan jaki a koma taiki ba, inda tun farko an dauki matakin hanasu
yin irin wannan tabargazar to da hakan bata faru ba. Don kuwa a gaskiyar lamari
babu addinin da zai saka ido ana masa cin kashi haka, kuma nayi imanin banda musulmai
suna da hakuri da tuni fitinar ta girmama.
Da haka nake Tur da wannan cin zarafin Manzon Allah(SAW)
da mujallar Charlie Hebdo dama sauran kafafen da ke aikata irin wannan badaqalar.
Ina kuma jawo hankulan 'yan uwa musulmai dasu cigaba da addu'ar Allah wadai su
kumayi tir da nuna damuwarsu karara. Sannan kuma shugabannin musulmai su hada kawunansu
su rika magana da murya daya tak don kawar da ire iren wadannan cin zarafin da
izgilanci da gangan dole ne musulmai su
kyamaci wannan badakalar su kuma sanya babbar alamar dakatarwa da zata hana cin
zarafin al'ummarsu, addininsu da kuma uwa uba Annabinsu (Tsira da Amincin Allah
su tabbata a gareshi). Allah ka qarawa Annabi daraja, wasila da fadila ameen.
Mudassir ya rubuto daga NTA Zariya
No comments:
Post a Comment