Thursday 27 July 2017

MATSAYIN WASU MATASAN AREWA DA MASU RAJIN WARGAZA KASA



 MATSAYIN WASU MATASAN AREWA DA MASU RAJIN WARGAZA KASA

DAGA:
MUDASSIR ALIYU YUNUSA
mudassiray@gmail.com

Sanin kowa ne a shekarar 1914 turawan mulkin mallaka suka hade yankin Kudu da  na Arewa da kuma Birnin  Ikko (Lagos colony) waje daya lamarin da ya haifar da samun gamammiyar kasar Najeriya. Tabbas  Arewa tun gabanin zuwan turawa yanki ne mai arzikin noma kiwo da cikakken tsarin mulki na sarautun gargajiya gami da tsarin ilimi, rubutu da karatu ta hanyar ajami, sanin kowa ne arewacin Najeriyarmu ta yau an same su al'adu, dabiu, tsarin shiga  da suturu na alfarma. Abin alfaharin shine yadda al'ummar yankunan kudu da arewa suka hade kansu don samar da yancin kai a shekarar 1960, suka kuma jajirce wajen bada gudummawarsu don cigaban kasar dugurungum. Sai dai abin takaicin da ya biyo  bayan shekara 6 shine da wasu gurbatattun 'yan kabilar Igbo wadanda aka fi sani da inyamurai karkashin jagorancin Manjo Chukuma Kaduna Nzeogwu da Manjo Emmanuel Ifejuana suka aiwatar da mummunan juyin mulki wanda ya bayyana tsagwaron kabilanci da bangaranci a fili wanda ya fara jawo batun kabilanci a Najeriya.  Juyin mulki da ya sake faruwa a tsakiyar shekarar 1966 ya kara dagula lamarin wanda yan kabilar inyamurai  suka bayyana aniyarsu ta ballewa daga Najeriya da nufin kafa jamhuriyar Biafra, lamarin da ya jawo yakin basasa na tsawon watanni 30 da yai sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyin mafiya yawan alummar Igbo dake yankin gabashin kasar nan. Bayan kusan shekaru uku da aka dauka ana gabzawa a inda jagoransu Kanal Emeka Ojukwu ya tsallake ya gudu shi ko Kanal Phillip Effiong ya zubda makaman yaki ya aminta da zama karkashin tarayyar Najeriya.
Abin lura anan shine yau shekaru arbain da bakwai da dakile yunkurin ballewar yankin na gabashin Najeriya sai dai har yanzu kudirin na nan a zukatan mafiya yawa daga cikin yan kabilar Igbo, duk da irin kawaici da yafiyar da yan arewa sukai musu musamman lura da kisan Firayin minista da firimiya da sauran manyan jagororin yankin amma abin ya zamo wata hanya ta nuna kyamatar yankin da kasar ta Najeriya wanda kuma an sami tsangwama da munanan kalamai da tozarci daga magoya bayan ballewar don kafa jamhuriyar Biafra, Sai dai ban ji manyansu da jagorinsu sun nuna kyamatar abun ba karara kamar yadda jagororin arewa suka zafafa ba akan matsayar gamayyar matasan arewa da suka fitar a farkon makonnan, hasalima sai tarba ta girma da wasu manyan yankin su kaiwa shi mutumin da yake ingiza maganar ballewar bayan samun beli.  Tabbas abun Allah wa dai ne a sami wani yanki ko wata kabila ta haifarwa da kasar nan tashin hankali ko batun wargajewa, sai dai in an bi ta barawo to abi ta mabi sawu. Ya zama wajibi gwamnoni, da yan majalisun arewa su aikewa da yan kabilar igbo sako da su guji tada zaune tsaye da sunan fafutukar ballewa daga Najeriya, saboda irin abinda sukewa yan arewa da cin mutuncin gwamnati shine dalilin da a cewar gamayyar kungiyoyin matasa na arewa yasa suka fitar da wannan barazanar.
Tabbas manyanmu na baya sun tsaya kai da fata wajen samarda hadin kan kasarnan tin gabanin samun yanci har zuwa lokacin yakin basasa. Wannan dalilin ne ya zamar mana wajibi mu rike irin kyakkyawan aikinsu kamar yadda yake a taken kasarmu " The labour of our heroes past shall never be in vein".  
Ina kira ga daukacin yan Najeriya musamman yan kabilar igbo dasu manta da wannan kudirin da aka dakusar dashi shekaru kusan hamsin da suka shude, mu hada kanmu don Samarwa kasarmu Najeriya cigaba mai dorewa, mu manta banbancin harshe, yanki, bangare addini don ciyar da kasarmu ta gado gaba.
A karshe gwamnonin arewa dana yankin igbo su zauna don takawa wannan matsalar birki gabadaya, don kuwa dole sai masu rajin ballewa sun dena maganganunsu na kawo rabuwar kai sannan sauran jamaar kasa za su dena maida martani.
Mudassir ya rubuto daga NTA Zariya.

No comments:

Post a Comment