Thursday 27 July 2017

ANYA KUWA ‘YAN MAJALISAR TARAYYA?



ANYA KUWA ‘YAN MAJALISAR TARAYYA?
DAGA
MUDASSIR ALIYU YUNUSA
       Dimokradiyya wani tsarin mulki ne da ya bada damar aiwatar da zabuka don zama shugabanni da wakilan jama’a a matakan gwamnati kama daga kananan hukumomi, jihohi da kuma tarayya. Haka kuma tsarin mulkin Najeriya ya rarraba matakan gudanar da mulki zuwa kashi uku, bangaren Zartarwa (Executive), masu yin doka (Legislature) da kuma sashen shari’a (judiciary). Kodayake a tsarin dimokradiyya ana gudanar da zabukan gamagari a matakan shugabanni  zartarwa da kuma yan majalisu ta hanyar zabe kai tsaye a karkashin jam’iyyun siyasa.
      Bisa la’akari da yawan jama’ar Najeriya lamarin da ya bada damar samar da tsarin majalisu guda biyu (Bicameralism) a matakin tarayya, Majalisar Wakilai (House of Representatives) da kuma Majalisar Dattijai (Senate House) irin yadda kasashen da suka cigaba a siyasa kamar Amurka da Birtaniya suka aiwatarwa. Babban aikin majalisa a siyasance bai wuce yin doka da oda, sanya hannu don amincewa ko rashin amincewa da wani kudiri na gwamnati, tantance duk wani abu da ka iya kawo cigaba ko rashin cigaba ga ‘yan kasa, da kuma sauran ayyuka da suka shafi wakilcin al’umma a gwamnatance. bisa  tsari majalisar dattijai ce kan gaba sai dai kuma majalisar wakilai na da tasiri fiye da babbar majalisar ganin cewa su suna wakiltar jama’arsu ne kai tsaye.
     A halin yanzu majalisun tarayya suna cikin rudani wanda ya samo asali daga zabi da nadin shugabannin da zasu jagoranci majalisar. Kodayake sanannen abune a majalisa samun sabani da rikici musamman wajen aiwatar da wata doka ko wani tsari wanda aka sami ra’ayoyi mabambanta  a kansa, sai dai a iya cewa halin da sabbin majalisun tarayyar Najeriya ke ciki na ciwa ‘yan kasar tuwo a kwarya ganin yadda ake sa ran samun canji da cigaba a siyasar kasar. Tun bayan faduwar jam’iyyar PDP da kuma gushewar mulkinta, jama’a da dama sun dokanta suga yadda jam’iyyar APC zata gudanar da salo da tsari na mulki musamman wajen wanzar da zaman lafiya, bunkasa tattalin arziki, dakile hauma-hauma, danniya, son kai da kuma tsabar cin hanci da rashawa da sukaiwa kasar katutu bisa la’akari da alkawuran da sukai wa jama’a a lokacin yakin neman zabe. Abin takaicin shine yadda ake samun sa-toka-sa-katsi a sabbin majalisun wanda ya samo asali a dalilin son kai da hankoron shugabanci da mukami a tsakanin wakilan. Lamarin da yai tsamari a majalisar wakilai kuma yai sanadiyyar dage zaman majalisar tsawon makwanni uku.
Abin tambayar anan shine kowa yasan ana samun rikicin ne ba don wani abu da zai cutar ko ya amfani talakawa ko kuma ya kawo cigaban kasa bane,a a sai don kawai tsabar son zuciya da tsantsan son biyan bukatunsu na kashin kai. Anya majalisun zasu maida hankali wajen tabbatar da abun da ya shafi cigaban kasa kuwa? Anya yan majalisun ba zasu rika fifita bukatunsu fiye da na wadanda suke wakilta ba kuwa? Anya kuwa  wannan son shugabancin ba suna yinsa bane don nemawa kansu madogara don cimma kudirinsu na siyasa anan gaba ba? Anya canjin da jama’a ke mafarki game da wannan sabuwar gwamnatin ta APC zai samu kuwa ganin yadda zababbun wakilan jama’a  suka fara nuna kansu akan abin da ake ganin cibaya ne a siyasa da salon mulkin adalci?
Haka kuma babban abin tsoron shine kada fa in tafiya tai nisa yan majalisun su rika fifita bukatunsu fiye da na yan kasa wadanda suka tsaya cikin rana da ruwa suka zabe su, kada kuma su rika yiwa muradan cigaba kafar ungulu don masu iya Magana sun ce juma’ar da za tai kyau tun daga laraba ake ganeta. Ina son tunatar da ‘yan majalisa cewar yan Najeriya fa sun zabi jam’iyyar APC ne bisa lura da irin zaqakurancinta na ganin an samu chanji da kuma samar da yanayin rayuwa mai kyau. Amma tabbas abin da ke faruwa a majalisun ka iya zama tasgaro ga wannan mafarkin ganin yadda suka nuna son mulki karara a bainar jama’a .
Ina kira da babbar murya ga kafatanin yan majalisun na kowacce jam’iyya da su farga su tuna da amanar da ke kansu na ‘yan kasa don tabbatar da cigaba mai dorewa, kodayake sun nemi afuwar yan kasa bisa irin kuruciyar da suka tafka a idon duniya amma a ganina neman yafiya bai wadatar ba matukar basu gyara halinsu ba sun kuma nuna zakakurancinsu wajen ciyar da kasar nan gaba ba.
A karshe ina son in kara tunatar da ku ‘yan majalisa cewar kuna sane da cewar kowannenku yana da babban nauyi akansa na jama’arsa wanda nayi imanin mutane ba za su yafe muku ba matukar baku sauke wannan nauyin ta hanyar da ta dace ba, wannan kuma zai faru ne kawai idan kuka manta da bukatunku na kashin kai kuka sanya bukatun al’umarku a gaba musamman a wannan lokacin da yake cike da sammatsi na neman waraka daga irin halin haula’i da wasu daga cikin shugabanni marasa kishi suka gadarwa kasar.  Wannan ne kadai mafitar da zata ceto kasarmu daga durkushewa ta kuma dora ta a turbar gaskiya da cigaba kamar yadda magabatan shugabanni na kwarai suka tsara.
Mudassir ya rubuto dag anta zariya

No comments:

Post a Comment