YUNKURIN KOYI DA HALAYEN SARDAUNA;
BA GIRIN GIRIN BA…….
DAGA
MUDASSIR ALIYU YUNUSA
Masu Magana na cewa “Wawaye adon tafiya”,
wannan haka yake bisa la’akari da tafiyar da ake aiwatarwa a yankin arewacin Najeriya
wadda take bukatar waiwaye domin kawata tafiyar a halin yanzu, tun bayan
rasuwar Mai girma Firimiyan tsohuwar jihar arewa Alhaji Sir Ahmadu Bello
Sardaunan Sakkwato (Gamji dan kwarai, Namiji uban yan boko) ake samun ja baya a
arewacin kasannan duk cewar an samu karuwa ta fuskoki da dama da suka hada da
yawan masu ilimi, wayewa, arziki sannan kuma an sami saukin aiwatar da wasu
abubuwa ba kamar lokacin da ba, amma sai dai babu ci gaba ta fuskar tattalin
arziki, siyasa da kuma jin dadi da walwalar jama’a musamman ga talakawan
yankin. Abin tambaya anan shine me ya jawo wannan koma bayan? Lallai idan muka
waiwayi irin halaye da dabi’un Marigayi Firimiyan zamu tabbatar da bukatar koyi
da su a wannan lokaci da yake cike da sammatsi ta fuskar jagoranci, zamantakewa
tattalin arziki da siyasa. Yana da kyau kwarai mu tuna irin abubuwan cigaba da yankin
arewa ya samu a lokacin Firimiya wadanda har a yau muna cin moriyar wasunsu da
suke nan kuma muke takaicin rashin wadanda suka durkushe daga cikinsu. Bama yan
arewa kadai ba wasu ma a yanzu dasu kasar take takama.
Misali,
a bangaren ilimi koda yake dama akwai ilimin addini, karatu da rubutu tun kafin
zuwan turawa amma ta fuskar ilimin boko kowa ya san irin babban aikin da Gamji
ya yiwa yankin arewa, an sami cigaba ta hanyar gina makarantun ilimin zamani
tun daga kan elemantiri, sakandire har zuwa kan manyan makarantun gaba da
sakandire kamar makarantar nazarin kimiyya, fasaha da harkokin yau da kullum ta
Kaduna (Kaduna Polytechnic) kai har ma
da jami’o’i irin su jami’ar Ahmadu Bello
dake Zaria (ABU) a yankin na arewa. Wannan ya ba arewacin Najeriya damar yin
gogayya da sauran sassan kasar duk da sun yi mana nisa ta fuskar ilimin zamani.
Ta fuskar tattalin arziki kuwa, kowa yasan
arewa akan Noma, Kiwo da sauran sana’o’in hannu irin su saka, kira, rini,
dinki, jima, dukanci, sassaka da sauransu, wadannan sana’o’in sun sami kula
sosai a lokacin Firimiya inda ya jajirce wajen zamanantar dasu domin su yi
daidai da wancan lokacin. An sami damar kafa Masaku a Kaduna, Funtua da Gusau;
Masana’antar sarrafa gyada; kamfanin Madara na Arewa wandanda suka taimaka
matuka wajen samar da ayyakan yi ga jama’ar arewa suka kuma bunkasa tattalin
arziki da daukaka darajar yankin arewa.
A bangaren cinikayya da kasuwanci Sardauna
ne ya samar da tsohon Bankin Arewa (Bank
of the North) da Kamfanin cigaban Nijeriya ta Arewa (Northern Nigerian Developmen Company) domin bunkasa harkokin
kasuwanci wanda sun kai makura wajen taimakawa al’ummar da tallafi don habaka
kasuwanci, noma, muhalli da cigaban jama’ar yankin. Dadin dadawa idan mu kayi
duba zuwa bangaren wayar da kan al’umma da ilimantarwa baza mu manta gidan
rediyon ta talabijin na Kaduna dana kano da sauran kafafen watsa labarai a
yankin wanda suke karkashin kulawar (Broadcasting
Comapany of Northern Nigeria) da kamfanin dab’i na arewa ba (Northern Nigerian Publishin Company), da
kamfanin jaridu irin su “New Nigerian”
da Gaskiya tafi Kobo wandanda suka taimaka matuka wajen wayarwa da ilimantar da
jama’a ta fuskar addini, zamantakewa, siyasa, kiwon lafiya, tattalin arziki da
sauransu.
Hakikanin gaskiya idan muka yi duba izuwa
ayyukan cigaba da Sardauna ya kawo arewa zamu tabbatar ya zarta sauran
takwarorinsa Firimiyoyin yankunan gabas da yamma na kasarnan, Sir Ahmadu Bello
ya zamo zakaran gwajin dafi a tsakanin su ta fuskar samar da jin dadi da
walwalar jama’a duk da cewar yankin da yake jagoranta yafi sauran yankunan
girman kasa, yawan jama’a, bambancin addini, kabilu, al’adu da dabi’u amma duk
da haka yankin ya samu cigaba fiye da sauran a wancan lokacin, tabbas wannan ya
samo asali ne bisa jajircewarsa bisa aldalci da kuma sanin hakkin talakawansa.
A halin yanzu abubuwa da dama sun
tabarbare a arewa inda yankin ke fuskantar babbar barazanar durkushewar
martabar da magabatan suka dora yankin akai. Ada jama’ar arewa suna cike da
walwala, jindadi da kwanciyar hankali, amma yanzu labarin ya sha bamban bisa
la’akari da halin kunci, masifar talauci wanda alkalumma suka nuna karfinsa
fiye da a sauran yankunan kasarnan. Haka kuma bincike ya nuna an fi samun yawan
cututtuka da ballewar annoba a arewa, sannan kuma yankin yafi ko ina a fadin
kasarnan yawan yara kanana marasa zuwa makaranta da suka dogara da aikatau a
gidajen masu hannu da shuni, yan siyasa da manyan jami’an gwamnati, wannan ya
samo asali ne ga irin sakaci, halin ko in kula da kuma rikon sakainar kashi da
jagororin arewa na wannan lokacin ke wa jama’arsu sabanin yadda Marigayi Sardauna
ya tafiyar da shugabancin ga mutanen arewa.
Yau shekaru 48 da durkushewar gwamnatin
yankin arewa, an kuma kasafta yakin zuwa jihohi 19 wandanda gwamnoni 19 ke
gudanar da sha’anin mulkinsu ba tare da la’akari da juna ba. To abin lura anan
shine yadda jagora daya tilo ya jagoranci daukacin jama’ar yankin kuma aka samu
cigaba mai amfani ga jama’a, ina ganin zai zamo da sauki a yanzu a wajen mutane
19 (Gwamnoni Jihohin Arewa). Alhamdulillah, a iya cewa su kansu jagororin suna
yabawa da irin salo da jagorancin Firimiya don kuwa sukan bada misali su da
kansu, kaga kenan a iya cewa ko sun gano bakin zaren ne sun kuma yi amanna da
cewar akwai matsaloli a yankin kuma dawo da martabar arewa bai yiyuwa sai anyi
adalci kamar yadda Sardauna yayi ada, sai dai mutane suna ganin ba’a nan gizo
yake sakar ba, babbar maganar itace yadda za’ayi amfani arzikin yankin wajen
dawo da martabar arewa ta fuskar yaki da talauci, bunkasa lafiya, inganta
ilimi, bunkasa aikin noma, farfado da masana’antu, cigaban ciniki da kasuwanci
da kuma kyautata siyasa da harkokin mulki da kuma uwa uba tsaron rayuka da
dukiyoyin al’ummar yankin.
Lallai in har za’ayi kokarin aiwatar da
abubuwan da aka gabatar a lokacin gwamnatin Firimiya Sa Ahmadu Bello to ba
makawa talakawan arewa zasu dara, yan kasuwa zasu sami cigaba sannan kuma
shugabannin arewa zasu sami nutsuwa gami da san barka daga wajen wadanda suke
jagoranta. Haka kuma arewa zata zamo abar misali, abar alfahari kuma abar
kwaikwayo ba ma kadai ga sauran yankunan kasarnan ba har ma ga sauran kasashen
duniya masu kishin talakawansu baki daya.
To amma fa hakan baza ta samu ba sai an sami
mutane na gari masu adalci, rikon amana, gaskiya, tausayi, juriya, hakuri da
kuma uwa- uba tsoron Allah. Sannan mu kuma jama’a mu basu hadin kai da goyon
baya mu kuma kyautata musu zato kuma muyi musu addu’a domin samun nasara ga
wannan muhimmin kudirin da ni, kai, ke zamu amfana da kuma yayanmu da jikokinmu
su mora a nan gaba.
MUDASSIR
ya rubuto daga NTA Maiduguri.