BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABA MUHAMMADU BUHARI
DAGA
MUDASSIR ALIYU YUNUSA
mudassiray@gmail.com
Da farko ina maka barka da dawowa
gida Najeriya bayan tsawon kwana 49 da ka yi a Qasar Birtaniya, da fatan alkhairi
kuma Allah yasa zakkar jiki ce. Bayan haka ya mai girma shugaban qasa abubuwa da
dama sun faru a lokacin da baka nan, wasu daga vangaren al'umma wasu kuma daga varin
gwamnati, nasan kana sane da hakan. Maganganu iri-iri sun ta yawo a cikin qasa musamman
a dandali da shafukan yanar gizo wadanda ke alaka da rashin lafiyarka da zamanka
a birnin Landan, wasu na maka fatan alkhairi a lokacin da wasu ke maka mugun baki.
Bayan wannan kuma nayi nazari na gano cewar akwai abubuwan ban mamaki da suka afku
wanda nake da shakku da alamar tambaya (?) akansu.
Ya mai girma shugaban qasa, a
lokacin tafiyarka an sami faxuwar darajar dalar amurka da aqalla kashi 5 cikin
100, lamarin da ya sanya darajar Naira ta karu kuma hakan ya kawo rangwamen wahalar
da dala ke jefa talakawan qasar nan. Wannan abu ne da ya kamata ka duba shi don
gano taqamaiman dalilin da ya kawo hakan tunda dama abune dake cikin burinka ganin
irin yadda gwamnatin ka ta damu da talakawanta.
An sami tsaiko na masu yiwa gwamnati
varna, musamman masu fasa bututun mai a wasu
yankunan don hana ruwa gudu, wanda hakan ya nuna akwai lauje cikin nadi dake bukatar
a warware nadin don gano abunda ke cikinsa. Haka zalika baa tava samun wata barazana
ko togashiya ga Mai girma Muqaddashinka ba ta inda yakan kai ziyarar aiki duk inda
yaso bagatatan ba tare da wani kalubale
daga wasu mutane a yankunan ba.
A vangaren samar
da wutar lantarki Kuwa kodayake ya danganta da yanayi da kuma lokaci amma a kwanaki
49 an samar da wuta gwargwadon hali har jama'a na san barka ga gwamnati. Wataqila
wannan ba zai rasa nasaba da dena fasa bututun mai dana makamashin da ake amfani
dashi wajen samar da wutar ba, sai dai shima wannan abin a duba ne mai girma shugaban
qasa.
Haka zalika a kowace
gwamnati akan sami mutanen kirki masu son cigaban qasa da kuma vatagari wadanda
a kullum sukewa gwamnati zagon qasa, maqarqashiya da kuma yin qafar ungulu ga cigaban
qasa don hana aikata abubuwan da suka dace, to a tafiyar nan taka fa anyi walkiya
wacce nake tunanin wataqila ta haska maka kowa, musamman ganin yadda wasu kafafen
watsa labarai suka bankaxo wasu sirri game da wasu makusantan gwamnatinka, koda
kuwa ba gaskiya bane to tabbas abin a duba ne tun yanzu don kada ya zama anyi fargar
jaji a gaba.
Mai girma shugaban
Qasa tafiyarka ta qara qarfafa haxin kan 'yan Najeriya musamman irin ximbin addu'o'in
da aka gabatar a gareka, wanda gungun jama'a dabam-dabam suka hadu waje daya kama
daga talakawa, masu mulki, masu sarauta, 'yan siyasa, 'yan kasuwa kuma abin sha'awar
shine yadda mabiya addinai suka riqa gabartar da addu'o'i a masallatai da majami'u
don samun lafiyarka. Wannan ya tabbatar da hadin kan jama'a ya kuma qara dankon zumunci a tsakanin mabambamtan
jama'ar qasar nan.
Mai girma shugaban
qasa akwai bukatar sanya wakilci mai kyau a mafiya yawan ayyukan gwamnatinka don
tabbatar da wanzuwarsu cikin gaskiya, tabbas kana da mataimaka da ma shawarta masu
nagarta, musamman mai girma Mataimakin shugaban qasa wanda yayi matuqar kokari a
lokacin da baka nan, wanda ya nuna cewar a shirye yake don tabbatar da cigaban kasa
a kullum, akwai masu taimaka maka wadanda ka nada su don baka Shawara, tabbas wasunsu
sunyi qoqari wajen wayarwa da jama'a Kai da kuma kwantar musu da hankali da lafazi
mai dadi a kafafen watsa labarai a lokacin da baka nan. Tabbas ire-iren wadannan
sune 'yan kishin qasa wadanda ya kamata ka riqe su don tallafawa tafiyarka ta sauya
yanayin qasarnan.
A qarshe ina baka
shawara da kai nazari mai zurfi akan dukan lamuran da suka afku bayan tafiyarka,
ka gano musabbabin faruwar hakan don tabbatar da su. Ina maka fatan alkhairi da
addu'ar Allah ya qara maka lafiya da karsashi ya kuma yi maka jagoranci wajen sauke
nauyin da ke kanka cikin sauki da hikima.
MUDASSIR ya rubuto
daga NTA Zariya.
No comments:
Post a Comment