Thursday 27 July 2017

GOBARA A KASUWANNI; LALLAI DA DALILI.



GOBARA A KASUWANNI; LALLAI DA DALILI.
DAGA:
MUDASSIR ALIYU YUNUSA
mudassiray@gmail.com

A ranar asabar da ta gabata ne al'ummar jihar Kano suka tashi da iftila'in babbar gobara a babbar kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi wacce akafi sani da kasuwar Sabongarin Kano, gobarar da ta shafe tsawon sa'o'i tana cinye dukiyoyi marasa adadi, wannan gobarar ta abku ne cikin dare wacce tai sanadiyyar konewar shaguna fiye da dubu uku(3000). Wannan lamari ya jefa daukacin jama'ar garin Kano da wajenta cikin yanayin alhini da damuwa kasancewar muninta da kuma yawan bayin Allah 'yan kasuwa manya da kanana da suka tafka mummunar asara. Gobarar dai ba'a taba yin irinta ba a tarihin gobarar kasuwanni a Kano.
Wannan lamari ya jawo maganganu dabam-dabam masu kyau da marasa kyau musamman a shafukan sada zumunta na jama'a (social networks), wasu na alaqanta abin da sakaci, kasawa, rashin gogewa da kuma rashin wadatattun kayan aiki masu inganci na hukumar kashe gobara ta kano wadanda suke da ofisoshi a Kofar Nasarawa, Dakata da kuma masu kula da filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano duk sun gaza kashe wutar kafin tai yawa, kai har ya zamto ana yekuwar neman agaji daga makotan jihar kamar Katsina, Kaduna, Jigawa da kuma neman taimakon jiragen sama na kashe gobara daga hukumomin gwamnatin Tarayya irinsu Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da kuma rundunar sojin sama ta kasa(Nigerian Air force). Kodayake wannan kiran al'umma ke yinsa watakila hukumomin basu bukaci hakan ba, koma dai meye ya faru tabbas hakan ba zai rasa nasaba da ganin irin gazawa da kuma rashin kayan aikin kashe gobara na zamani da hukumomin suka rasa wajen kashe wutar ko hanata yaduwa a cikin kasuwar kamar yadda kasashen da suka cigaba irinsu Amurka da Kasar Sin suka nuna a lokacin da irin wannan masifar ta afku akansu.
A wani kaulin kuma Jama'a na jingina laifin ga rashin kula wajen ta'ammali da wayoyin wutar lantarki da ake hadawa daga wannan shagon zuwa wancan da yan kasuwar da ma'aikatan kamfanin wutar lantarkin ke yi a cikin kasuwar wanda ka iya jawo tashin wutar a kowanne lokaci. Kodayake naji kuma ana batun cewar babu wutar lantarki a layin da yake kai wutar cikin kasuwar. Haka zalika ana zargin ko wasu mutanen ne masu son dakile cigaban kasuwanci a jihar Kano ke cinna wutar don durkusar da hada-hadar cinikayya da akasan Kano dashi musamman ganin yadda a baya kadan ma babbar kasuwar singa dake Kanon ta ci wuta inda nan ma aka sami mummunar asarar dukiya mara adadi.
Har ila yau dai wannan masifar wasu na ganin duk maganganun mutane shaci fadi ne lamarin daga Allah ne don ta zamto izina ga wasu yan kasuwa masu tauye hakin Allah na zakka, tauye mudu, sanya farashi mai tsada, takurawa al'umma ba tare da dalili ba musamman abinda ke faruwa na tashin farashin dalar Amurka wanda hatta wasu yan kasuwar da basa ta'ammali da ita sun zabgawa kayansu farashin da ya janyo wahalhalun da jama'a ke ciki a yanzu su kuma danganta tsawwalawar da tashin dalar.
Wadannan duk maganganu ne da ke zagaye a tsakanin al'umma musamman a kafafen soshiyal netwok, duk da ansan dole akwai dalilin afkuwar lamarin, sai dai wannan lamarin Allah kadai ya barwa kansa sanin hakikanin dalilin afkuwarsa wanda muke neman tsari da afkuwar kwatankwacin irinsa a gaba.
Ina son nayi amfani da wannan damar na shawarci gwamnati da jama'a akan wannan kaddarar: da farko ya kamata gwamnati ta inganta harkar taimakon gaggawa musamman hukumar kashe gobara wato (Fire Service), ya zama wajibi a samar musu kayayyakin aiki na zamani in ta kama har jiragen sama a samar musu musamman idan akai la'akari da girman gari kamar Kano. Dadin dadawa ya kamata a samar musu da horo mai zurfi na kashe gobara koda kuwa za'a kaisu kasashen da suka cigaba don koyar dasu dabaru da sanin makamar aikin taimakon gaggawa da kashe annobar gobara.
Shawara ta ga Jama'a kuma itace a duk lokacin da irin wannan masifar ta afku to mu kiyaye mu kuma iya bakinmu, mu roki Allah kiyayewarsa madadin muyi ta maganganu marasa tushe. Mu sani cewar na daga cikin jarrabawa Allah ya kaddaro maka afkuwar wani abu mai kyau ko maras kyau don a jarrabi imaninka. Saboda haka ya zama wajibinmu ne mu rika taka tsantsan da kalamanmu, mu tuba zuwa ga Allah mu kuma gyara halayenmu da dabi'unmu.
A karshe ina kira ga gwamnatoci kama daga tarayya har zuwa kananan hukumomi dasu dubi wadanda wannan masifar ta afkawa da idon tausayi don samar musu da wani shiri da zai tallafa musu ya kuma rage musu radadin da suka tsinci kansu a cikin dare daya, hakan ka iya taimakawa wajen sake bunkasa harkar kasuwanci a yankunan  da irin wannan masifar ta faru garesu. Mutanen gari ma na da tasu gudummawar da zasu iya bayarwa ta hanyar sanya gidauniyar neman taimako a cikin unguwanni da masallatai na Jumma'a dana hamsu salawat  kai har ma da majami'ai na mabiya addinin kiristanci don tallafawa wadanda suka yi asara gwargwadon hali kasancewar asarar ba kadai musulmai ta shafa ba har da kiristoci.
Ina sake mika jaje na da alhini ga dukkan wanda wannan iftila'in gobarar ya shafa. Allah ya tsayar haka ya kuma mai da mafi alkhairinsa. Ameen
MUDASSIR ya rubuto daga NTA Zariya.

No comments:

Post a Comment