Thursday, 27 July 2017

JARRABAWAR UTME; AKWAI SAKE A SABON TSARIN



JARRABAWAR UTME; AKWAI SAKE A SABON TSARIN

DAGA:
MUDASSIR ALIYU YUNUSA
mudassiray@gmail.com

    Sabon tsarin jarrabawar shiga jami'o'i da manyan makarantun gaba da sakandire ta UTME wacce hukumar samar da guraben karatu a manyan makarantu ta kasa wato JAMB ke shiryawa da ake gudanarwa a halin yanzu yazo da matsaloli da dama.
A da akan gudanar da jarrabawar ne cikin wasu sa'o'i da ba su wuce goma ba a cikin wuni daya  wanda haka shine tsarin da aka sani tun asali, sai da a halin yanzu za'a dauki tsawon kwanaki goma ne ana gudanar da jarrabawar, Kodayake ana samun matsaloli a wancan tsarin musamma daga baya da ake samun yawan daliban dake rijista don rubuta jarrabawar wanda hakan yasa hukumar rarraba daliban a cibiyoyinta dake fadin kasar nan, akan tura yara jihohi daban daban don rubuta jarabawar. Hakan yana cusgunawa yaran sannan yana haifar da rashin kwanciyar hankali ga iyaye musamman ga masu 'ya'ya mata, sai dai duk da hakan ana daurewa a tafin.
A halin yanzu hukumar ta JAMB ta kirkiro sabon salon daukar jarrabawar ta hanyar yanar gizo (online) bisa amfani da na'ura mai kwakwalwa da suke kira Computer Base Test (CBT). A wannan tsarin sun rarraba daliban kashi kashi wanda zasu dauki fiye da mako guda suna gudanar da jarrabawar sabanin a lokutan baya da ake yi a wuni daya. Kodayake a iya cewa sauya salon daukar Jarrabawar abu ne mai kyau musamman ganin yadda zamani ya zo da cigaban fasahar sadarwa ta yanar gizo (internet), sai dai da alama sun bar sauran rina a kaba wacce zata janyo jangwangwama musamman ga daliban dake da kudirin shiga jami'a ko manyan makarantu.
Babbar matsalar itace rashin kwakkwaran shiri daga hukumar, misali daga cikin matsalolin sun hada da rashin kyakkyawan yanayi ga daliban inda wasu daliban da dama ba a garuruwansu suke jarrabawar ba, ana tura su garuruwa masu nisa wasu kam basu da dangin iya ba na baba, basu san kowa ba,  Hakan na tilasta musu neman wuraren kwana a garurwan ko kuma su hakura da jarabawar dungurungum.
Abun takaicin kuma shi ne a ranar farko an saka lokacin fara jarabawar karfe shida ga yan farko amma har zuwa karfe daya basu fara ba, sannan kuma ana sa ran rukunai uku ne zasu yi jarrabawar a rana daya. Haka kuma rashin ingantaccen netwok ya bada gudummawa wajen dagula shirin, don wasu yaran sun koka musamman ganin yadda lokutan da aka ware ke cigaba da tafiya amma rashin network kan kawo tsaiko ga daliban, haka kuma matsalolin rashin tabbas na bayyanar sunayen wasu daliban a cibiyoyin da aka shirya tana ci musu tuwo a kwarya. Wadannan da kuma wasu matsalolin sun sanyaya gwiwar yara sun kuma kashe musu karsashi don cigaba da neman ilimi. Tun a ranar farko yara da dama musamman wadanda suka zo daga nesa sun hakura sun koma garuruwansu don neman sauki.
 Da farko jama'a sun yi murna da shigo da sabon tsarin don ana ganin sauki ne ya samu musamman ganin yadda fasahar sadarwa ta zamani ke saukaka abubuwa ta hanyar gudanar da su a ko ina ba sai an tafi wani waje mai nisa ba.
Tabbas akwai bukatar duba wannan lamarin ganin yadda yake cike da rudani musamman ga daliban. Gwamnatoci musamman na jihohi su duba wannan tsarin da idon basira, su kuma bincika yawan yaransu da sukai rijista shin duka sun sami damar daukar jarrabawar? Masu ruwa da tsaki da kuma kungiyoyi masu rajin kawo cigaban ilimi su farga don kawo gyara akan wannan tsarin cikin gaggawa. Ilimi dai shi ne gishirin rayuwa, sannan cigaban kowacce al'umma baya samuwa sai an ilimantar da yara wadanda ake tunanin su zamo manya ko kuma jagororin gobe, don haka ya zama wajibi a rika lura da sabgoginsa tun daga matakin farko har zuwa jami'a.
A karshe ina fata hukumar JAMB zata saurari korafe korafen dalibai da jama'ar gari wajen gaggauta kawo masalaha musamman ga ire iren matsalolin da aka fuskanta don bada tasu gudummawar wajen inganta ilimi da cigaban al'umma.

MUDASSIR ya rubuto daga NTA Zariya.

No comments:

Post a Comment