Thursday, 27 July 2017

KASAFIN KUDIN 2016; DAYA TAMKAR DA GOMA



KASAFIN KUDIN 2016; DAYA TAMKAR DA GOMA
DAGA:
MUDASSIR ALIYU YUNUSA
DA
AMIR BAGWANJE
Kasafin kudi abune da gwamnatocin Jihohi da Tarayya suka kasance suna aikatawa a duk shekara don samar da ayyuka da kudire-kudiren cigaban al’umma da kasa baki daya. An dade ana aiwatar da kasafin kudi a Najeriya sai dai a iya cewa ba’a taba samun yanayin da jama’a suka maida hankali da bibiyar kasafin kamar na bana (2016). Dalilan rashin maida hankalin da kuma nuna halin ko ina kula da lamarin kasafin kudin bai rasa nasaba da irin halayyar shugabanni da jama’ar kasar ba nayin wasarairai da  kudiri da alkawuran da ‘yan siyasa kan dauka gabanin zabe. Duk da yake akan nuna rashin kulawar ne bisa rashin tabbas da kuma rashin tabbatuwar ayyukan da aka tsara a cikin kasafin kudin kasar a baya.
Tun bayan komawar najeriya kan turbar dimokradiyya a shekarar 1999, an shigar makudan kudade don aiwatar da ayyukan da aka ambata a kasafin kudi na shekara, misali idan muka duba shekaru 5 baya (daga 2010 zuwa 2015) zamu ga a 2010 an ware kudi har Naira tiriliyan 4.4; 2011 Naira tiriliyan 4.2; 2012 Naira tiriliyan 4.749; 2013 Naira tiriliyan 4.92; 2014 Naira tiriliyan 4.962 sai kuma 2015 Naira tiriliyan 4.4. Abun lura anan shine ina aikace-aikacen da aka wanzar da kudaden da suka tasamma zunzurutun kudi har Naira Tiriliyan 20 a shekaru 5? Ba za’a iya cewa babu komai kwata-kwata na cigaba a kasa ba tunda an sami cigaban darajar alkaluma na kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida (GDP) lamarin da yasa Najeriya ta zama kasar da tafi kowacce karfin tattalin arziki a nahiyar afrika a shekarar 2014, sai dai ba anan gizo yake sakar ba tunda hakan bai chanza halin kuncin da talakawan kasar ke fama dashi ba musamman talauci da bambance- bambancen rayuwa tsakanin masu hannu da shuni da kuma talakawa. Duk hakan ta faru ne sakamakon bakar sata, barna da irin ta’annatin da wasu ‘yan siyasa da kuma jami’an gwamnati suka tafka wand ko shakka babu ya janyo koma baya ga kasar ta fuskar tattalin arziki da zaman takewa.
Abubuwan da ya kamata ayi la’akari dasu wadanda suka nuna koma bayan kasar nan basu wuce matsanancin karacin wutar lantarki da kayayyakin more rayuwa da suka hada da ingantattun hanyoyin mota, asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya, makarantu, matsalar zaman kasha wando da rashin aikinyi ga matasa, matsalar tsaro a yankunan Arewa maso Gabas, Kudu maso Kudu, da kuma barazanar ballewa da kafa jamhuriyar Biafra wadanda ke barazana da tarnaki ga zaman lafiya, hadin kai da kuma dunkulewar kasar a matsayin tilo.
Ganin irin yadda akewa kasafin kudi rikon sakainar kashi ta hanyar wanzar da kasa da kashi 50 cikin 100 yasa gwamnatin buhari a wannan shekarar 2016 ta fitar da sahihin kasafin kudi wanda ya dau hankalin jama’a na zunzurutun kudi har Naira Tiriliyan 6.06 wanda ya zarta na kowacce shekara tun dawowar dimokradiyya. Kodayake kasafin ya sami tsaiko saboda wasu dalilai da suka hada da almundahanar ma’aikata (padding), jinkirin tantancewa da tabbatarwa daga yan majalisa da bangaren  zartaswa musamman saboda ana zargin cire wasu manyan ayyuka daga cikin kasafin (kamar aikin layin dogo daga Birnin Ikko zuwa Calabar, da kuma chanza fasalin ayyukan mazabun ‘yan majalisa da ake kira constituency projects), lamarin daya jawo jeka-ka-dawo da kasafin tsakanin bangarorin biyu, kodayake hakan na da tasiri musamman a cigaban dimokradiyya da kasa baki daya wanda da dama a baya hakan bata faruwa saboda kowanne bari ana biya masa bukatar son ransa, don kuwa a gaskiayar lamari shugabannin da suka shude suna aiwatar da kasafin kudin ne don kawai cika umarni da tanadin tsarin mulki ya tanada ba don ya zamar musu wajibi su aiwatar da kasafin don ciyar da kasa gab a ba.
Abun tambayar anan shine me yasa kasafin bana (2016) ya dau hankulan kafatanin al’ummar Najeriya? Ko don jaama’a na ganin yanzu ne za’a wanzar da gaskiya tunda shugaba Muhammadu Buhari mutum ne mai nagarta da bin diddigin gaskiya don tabbatar da ayyukan da aka zayyana a cikin kasafin kudin? In ko hakane tabbas ko a nan an sami chanji mai kyau da zuwan Shugaba Buhari wanda jama’a kewa ganin ba cuta ba cutarwa, kuma ba gar aba zago wajen saisaita kasarnan bisa turbar cigaba mai dorewa. Kodayake mutane da daman a ganin zai wuya kasafin kudin ya samu nasara kamar yadda ake tunani musamman ganin yadda farashin gangar danyen man fetur ta fadi wanwar a kasuwar duniya ganin yadda man fetur ya zama arzikin da Najeriya take tinkaho dashi wajen samun kudin shiga mai tsoka don wanzar da kudire-kudirenta. Sai dai ni ina ganin babban abin farin ciki anan shine akwai hanyoyin samun kudaden shiga wadanda zasu tallafa wajen samun nasarar kasafin kudin,  tunda a halin yanzu matsalar sata da wasoso da kudin gwamnati ta kau to akwai yiwuwar hukumomin da ke da alhakin Tarawa kasar kudin shiga irinsu Hukumar tattara harajin cikin gida (FIRS), Hukumar Yaki da fasakwauri ta kasa (Custom Serv), hukumar kula ta tashoshin jiragen ruwa (NPA), Hukumar kula da kafafen sadarwa ta kasa(NCC), hukumar kula da shige da fice ta kasa(Immigration) da sauransu zasu taka mihimmiyar rawa ganin yadda hakan zai zamto na farko wajen samar da kudaden da ake tunanin mai kadai ke samarwa. Tabbas tunda matsalar rashawa da cin hanci da satar kudaden al’umma ta ragu akwai zato mai kyau a batun wannan kasafin na bana wanda ake wa ganin DAYA TAMKAR DA GOMA.
A karshe ganin yadda gwamnatin Buhari ta maida hankali wajen kasafin kudin nan aban nasan zasuyi iya bakin kokarinsu don tabbatar da ayyukan cikin gaggagwa don rage radadin wahalar da ‘yan Najeriya ke fama da ita a halin yanzu wadanda  suka sha rana suka sha wuya don tabbatar da zaben wannan gwamnatin mai adalchi don ciyar da kasar nan gaba ta hanyar samar da chanji mai amfani da nagarta.

No comments:

Post a Comment