Thursday 27 July 2017

CIGABA A JIHAR KADUNA; RUSAU KO RUDAU?



CIGABA A JIHAR KADUNA; RUSAU KO RUDAU?
DAGA
MUDASSIR ALIYU YUNUSA
mudassiray@gmail.com

Sanin kowa ne lokacin turawan mulkin turawan mallaka garin kaduna shine magudanar tafiyar da sha'anin mulkin mallaka a yakin arewacin kasar nan, a Kaduna Gwamna Gwarangwam mai kula da yankin arewa ya zauna kuma dukkan Rasdan Rasdan na yankunan arewa nan suke haduwa don tattauna batutuwan da suka shafi lardin. Haka abin ya cigaba bayan an sami 'yanci a shekarar 1960 kadunan dai itace cibiyar mulkin jihar Arewa wacce firimiya ke jagoranta. A wadancan lokutan garin na kaduna ya sami tagomashi ta fuskar cigaban tattalin arziki, tsare tsare, siyasa da kuma ayyukan raya kasa da walwalar jama'a, sai dai a iya cewa bayan anyi jiha jiha a Najeriya wasu garuruwan a yankin arewa sun sami cigaba fiye da ita ta fuskoki da dama. Misali garin Abuja dake kudancin kaduna ya sami cigaba bayan zabarsa da akai don zama babban birnin gudanar da mulki na tarayyar Najeriya. Kodayake a iya cewa wannan cigaban gwamnatin tarayya ce ta kawo shi amma in akai duba izuwa garin Kano wanda ke karkashin Kaduna tun zamanin mulkin turawa da kuma lokacin firimiya har zuwa lokacin da aka kirkiri jihohi a tarayyar Najeriya, sai dai a yanzu cigaban da jihar Kano ta samu yasa ta zamto birni na farko a arewacin kasar nan da ya shahara ta fuskar cigaban kasuwanci, tattalin arziki, yawan jama'a, siyasa, fadin mulki da kuma tsarin gine gine masu kayatarwa. Haka zalika jihar katsina wacce take cikakkiyar 'ya ga Kaduna a halin yanzu ta zarta mahaifiyarta musamman ta fuskar bunkasa ilimi, hanyoyi da kuma samar da kayan more rayuwa da suka hada da ruwan sha da gidaje. Abin tambayar anan shi ne me ya jawowa jihar kaduna wannan koma bayan wanda wasu daga cikin 'ya'yanta da kannenta suka zarce mata wasu kuma ke kokarin yin kafada da kafada da ita da fuskar cigaban jama'a? Ni dai amsar da zan iya bayarwa a ganina bai wuce irin wasarairai da rikon sakainar kashi da jagororin jihar su kai tun bayan mutuwar Sir Ahmadu Bello. Gwamnatoci da dama sun shude amma basu mai da hankali wajen cigaba da gina jihar ba kamar yadda Firimiya ya fara ba.
A halin yanzu an sami chanjin gwamnati a jihar kuma sabuwar gwamnatin tazo da kudirin sake gina jihar ta kaduna ta fuskoki daban daban. Sai dai a ganina zakaqurancin samar da cigaba cikin gaggawa ba zai haifar da xa mai ido ba, ko da kuwa za'a sami cigaban to zai iya zama na mai hakar rijiya. Abin da yasa nace haka shi ne tunda sanin kowa ne jama'ar Najeriya sun sha fama da tsanani da kuncin talauci na tsawon lokaci musamman bakar wahalar da jama'a suka sha a shekaru 16 na mulkin PDP, sai dai abin da sabuwar gwamnati a jihar kaduna ya kamata ta fara aiwatarwa shine ayyukan farfado da jama'a daga wahalar rayuwa da bunkasa tattalin arziki. Misali a ganina kafin ace gwamnatin jihar kaduna ta fara rushe rushe ya kamata ta fara samarwa jama'a musamman matasa ayyukan yi ta hanyar farfado da masana'antu manya da kanana da kuma uwa uba samar da ruwan sha da fadada hanyoyi musamman a garin zaria wanda yake fama da karancin abubuwan more rayuwa duk da irin tumbatsarsa. Abun da gwamnatin jihar ke gudanarwa na rushe gine ginen da akai ba bisa qa'ida a cikin makarantu da ma'aikatun gwamnati abune mai kyau ko don tabbatar da yanayin tsarin kasa mai  kyau, sai dai kuma ina kira ga gwamnatin jihar kaduna da ta kula ta kuma rika sara tana duban bakin gatari sannan kuma ta tuna irin halin da gwamnatin da ta shude ta jefa mutanen kasar nan sannan alkawuran da APC ta dauka na samar da sauyi mai kyau na cigaban jama'a, lallai akwai bukatar ceto jamaa daga wahala ba a kara turasu cikin taraddadi ba.
Na zaga wata unguwa dake kusa da dakin karatu da kuma ofishin hukumar kashe gobara duk a garin Zariya wanda gwamnatin jihar Kaduna ta sawa alama don mayar da gurin fili fetal!  Tabbas bazan iya kididdige yawan gidajen da za'a rushe ba, amma abinda tunani na ya fara karanta min shine: koda ba bisa ka'ida suke ba amma ya akai gwamnati ta bari har gurin ya zama katafariyar unguwa haka? me gwamnati za tai da wajen? shin gwamnati zata samar musu da wani matsugunin ne ko zata biya su diyyar da zasu gina sabbin muhalli?  In ba haka ba anya rusau ba zai zama rudau ba kuwa?  ganin yadda gwamnati ta rude wajen tayarwa da talakawan da ke fafutukar neman abinda zasu saka a bakinsu,vTalakawan da akai musu romon baka da alkawuran samun canji da samar musu da walwalar rayuwa, talakawan da sukai ruwa suka tsaki, sukai uwa sukai makarbiya akan sai an sami chanji gwamnati a dukkan matakan gwamnati.
Ni kam a iya sanina na ilimin tattalin arziki (economics) akwai wani tsari na samar da jindadi da walwala (welfare theory) da yake cewa samarwa mutane sama da biyu jindadi shi ne abin da ya dace koda kuwa mutum daya tilo zai sha wahala, amma a wannan unguwar nasan aqalla sama da mutane dubu zasu tagayyara akan abinda da ba'a san me gwamnatin za tai da wajen ba, amma matukar ba'a samarwa jama'a kayan more rayuwa ba to bai kamata kuntata musu ba.
Shawarata ga  gwamnatin jihar Kaduna itace  ta himmatu wajen samarwa talakawanta ayyukan yi da abubuwan more rayuwa kafin akai ga rushe rushe da kuma tayar da jama'a daga matsuguninsu. Wannan ne kawai zai sa jama'a su san cewar sun sami chanji su kuma sami nutsuwa da gwamnati. Kuma ina tunatar da jagororin gwamnati dasu tuna lokacin yakin neman zabe inda su kaiwa jama'a alkawura da dama musamman wadanda zasu kawo cigaba mai dorewa, kodayake a jihar Kaduna akwai maganar rusau tun gabanin zabe amma bai kamata ya zamto aikin da zai gabaci manyan ayyukan more rayuwa da aka fi bukatarsu don chanza rayuwar al'umma ba.
A karshe ina kira ga jama'a dasu bawa gwamnatoci hadin kai wajen yaki da rashin da'a da sauran abubuwan da basu dace ba ita kuma gwamnati ta tabbatar da adalci da rikon amana a tsakanin alumma.
Mudassir ya rubuto daga NTA Zariya.

No comments:

Post a Comment