A DUBA TITUNA DA
HANYOYIN KASAR NAN
DAGA:
MUDASSIR ALIYU
YUNUSA
mudassiray@gmail.com
Sufuri wani abune mai matukar mihimmanci a rayuwar al'umma,
cigaban kowacce kasa baya samuwa sai an sami ingantattun hanyoyin sufuri kama daga
hanyoyin mota, layin dogo, sufurin jiragen sama dana ruwa da kuma sauran hanyoyin
da ke taimakawa al'umma wajen zirga zirga a cikin kasa.
A Najeriya mafiya yawan jama'a sun fi amfani da Sufurin
motoci wajen gudanar da tafiye tafiyensu na safarar kasuwanci, neman ilimi,
zimunci da sauran ayyuka da sabgogin rayuwa. Sai dai a halin yanzu lalacewar manya
da kananan hanyoyin mota a fadin kaaarnan ta zamo babbar annoba da kalubale musamman
yadda yawa yawan titunan kasar sun tsufa wasu sun mutu murus wanda hakan ke da alhakin
kawo munanan hadura dake jawo asarar rayuka, lafiya da dukiyoyin jama'a maras adadi.
Wannan al'amarin ya kasance abun damuwa kuma abun takaici musamman ganin yadda Allah
ya huwacewa kasar nan mamakon arziki wanda ya kamata ace tun tsawon shekaru 56 maganar samar da ingantattuun
hanyoyin sufuri musamman tituna an gama dasu, sai dai kash! Barna, wawaso da kuma
tsananin son zuciya na jagororin kasar yasa ake
fuskantar halin kunci da tabarbarrewar
al'amura a halin yanzu.
A dukkan bangarorin kasar nan yawa yawan hanyoyin da
suka hada manyan garuwa da jihohi suna matukar bukatar gyara ko sabuntawa. Misali
a arewacin Najeriya hanyoyin da suka hada da Gombe zuwa Yola, Kaduna/saminaka
zuwa Jos, Kano-Zariya-Kaduna har zuwa Abuja, Zariya -Funtuwa - Gusau zuwa Sokoto
da sauransu suna bukatar agajin gaggawa daga gwamnatin tarayya da ma na jihohi don
ingantasu. A shekarun baya hukumar dake da alhakin kula da gyaran tituna(FERMA)
tana iya kokari wajen yin kwaskwarima da
garanbawul a manya da kananan tituna a fadin kasarnan, sai dai yanzu kam
ba amo ba labarin ta lamarin da wasu Kewa
kallon gazawar gwamnati wajen gina sabbin hanyoyi, gyaran tituna da gadoji.
Shawara ta anan itace tunda yanzu Kasar na fama da matsalar
tabarbarewar tattalin arziki wanda ake ganin ya jawo rashin gabatar da wasu ayyukan cigaba,
me zai hana gwamnati ta dawo da tsarin karbar harajin hanya da ake bayarwa ada
(Toll Gate) don a rika amfani da kudaden don gyaran hanyoyin. Gwamnati da hadin
gwiwar kungiyoyin masu amfani da tituna su sanya ido wajen tattara kudaden da aka
karba a hannun masu ababen hawa musamman a manyan hanyoyi don tabbatar da ana gyara
da kula da titunan akai akai. Wannan zai sai dole a rika gyaran hanyoyin lokaci
zuwa lokaci wanda rashin yin hakan ka iya jawo tuhuma daga masu ababen hawa
dake amfani da hanyar, hakan kuma ka dakile daukar lokacin da ake ba tare da kula
da titunan ba.
A karshe ina kira ga gwamnatocinmu dasuyi gaggawar kaiwa
manyan titunan kasar nan agajin gaggawa don rage yawan afkuwar hadura a dalilin
rubewar tituna.
MUDASSIR ya rubuto daga NTA Zariya.
No comments:
Post a Comment