MARIGAYI NAJIB
ALIYU YUNUSA
(1982 - 2012);
DAN UWA RABIN JIKI.
DAGA:
MUDASSIR ALIYU
YUNUSA
NTA ZARIYA
mudassiray@gmail.com
Tabbas dukkan mai rai mamaci ne kamar yadda Allah madaukakin
sarki ya bayyana mana a cikin littafinsa mai tsarki, haka kuma hausawa na cewa
"duk wanda ya sanya taguwar rayuwa to dole mutuwa zata tube ta ko ba dade ko
ba jima". Wannan ya tunamin da amshin wakar rayuwa ta Fati Rayuwa inda take
cewa " Rayuwa tana faruwa wucewa take kamar ba ayiba". Wannan shine yadda
Allah ya tsara, shi yasa a cikin suratul mulk ya ambaci halittar mutuwa a farko
kana ya ambaci halittar rayuwa daga bisani.
Mutuwa nada ciwo, takan sanya shiga rudani da dimuwa
tsawon lokaci musamman ga makusantan mamacin. Tabbas na gaskata hakan shekaru 5
da suka shude sakamakon rashin dan uwana na jini na jika wanda akasarin rayuwata
tare mukayi tun muna yara tun bamusan ciwon kanmu ba balle na jiki. Marigayi Najib
shine tsara na da na bude ido na gani a tare dani, komai na yarinta tare muke gabarta
dashi kama daga cin abinci, wanka, wanki, wasa, bacci da zuwa makarantar allo da
islamiyyar dare da yamma. Rana daya aka sanya mu a makarantar firamare, lokaci daya
aka kaimu cikin makaranta daya, idan an fito
tara(9) tare muke cin abinci sannan muyi tsalle tsalle a lokacin takaitaccen hutun
daukar darasi (short break), sannan in an tashi mu hallara a waje daya don jiran
me kaimu gida. Haka abun ya cigaba da gudana idan muka dawo gida, daki daya muke
kwana tsawon shekaru 25 har zuwa lokacin da na tafi bautar kasa a Jihar Borno, shi
kuma jim kadan ya sami sauyin wajen aiki daga Kano zuwa Abuja.
An haifi Marigayi Najib Aliyu a unguwar Tarauni dake
karamar hukumar birnin kano( yanzu karamar hukumar Tarauni) a ranar 19 ga watan
mayu, 1982. Ya fara karatun muhammadiyya a makarantar allo ta mallam Bature dake
Tarauni da kuma makarantar islamiyya ta da'awa dake Sulaimanu Crescent duk a cikin
Kano. Ya shiga makarantar firamare ta Magwan Model Primary School a 1990, bayan
kammalawa ya shiga karamar sakandire dake Sabuwar Kofa Kano, daga nan ya wuce kwalejin
Rumfa dake Kano inda ya samu shaidar kammala sakandire ta SSCE a shekarar 2001.
Ya samu gurbi a kwalejin ilimi ta gwaunatin tarayya dake Kano (FCE Kano) a wannan
shekarar inda ya sami shaidar NCE a sha'anin kasuwanci (Bussiness Admin) a 2005.
Ya fara aiki a 2007 da gidan man Sani Brothers Petroleum na rukunin kampanin Sani
Brothers Transport Ltd, a matsayin mai kula da kudi (Cashier), ya samu cigaba inda
ya zama shugaban gidan man na dai kampanin a babban birnin tarayya Abuja, mukamin
da ya rike tsawon shekaru 4 har zuwa lokacin rasuwarsa. Ya kuma ci gaba da
karatunsa na digiri a jamiar Abuja dake Gwagwalada. Marigayin ya taimakawa jama'a da dama
wajen yi musu hanyar samun aiki a gidajen man kamfanin dama sauran wurare.
Marigayi Najib mutum ne na jama'a me girmama na gaba
dashi, mai mutunta abokansa, mai barkwanci ga yara, mai tsananin sada zumunta ga
yan uwa na birni da na kauye sannan kuma uwa uba matashi ne mai riko da addini.
Shakuwarmu dashi takai makura don duk da ina aikina amma bai kula da hakan ba don
a duk lokacin azumi sai ya bani kyalle na tufa don yin dinkin sallah. Haka zalika
a lokuta da dama in zai zo ganin gida daga Abuja, nakan jira shi a Kaduna ko Zaria
har sai yazo ya dauke ni zuwa Kano, lamarin dake bamu damar tattauna batutuwan da
suka shafe mu da 'yan uwanmu da ma hirar rayuwa.
Labarin rasuwarsa ta tayar da hankulan 'yan uwa, abokan
karatunsa da na aikinsa, makotansa, malamansa da sauran jamaar gari.
Ya rasu ranar juma'a 18 ga watan Mayu, 2012 a dai
dai lokacin da jama'a ke amfana da dimbin kyautatawarsa a garesu. Ya amsa kiran
ubangijinsa ya bar mata daya da yaro daya (Ahmad Najib), iyayensa da yan uwansa
maza da mata 19. Allah ya gafarta masa ya kyautata namu zuwan ya kuma albarkaci
abinda ya bari. Yan uwa da abokai kuma Allah ya kara mana hakuri da juriyar wannan rashin. Amin.
MUDASSIR
ya rubuto daga NTA Zariya.
No comments:
Post a Comment