Thursday 27 July 2017

GURBACEWAR BIKIN AURE A KASAR HAUSA.



GURBACEWAR BIKIN AURE A KASAR HAUSA.

DAGA:
MUDASSIR ALIYU YUNUSA
NTA ZARIYA
mudassiray@gmail.com


"Abin fahari abin sha'awa al'adunmu 'yan Kasar Hausa. Kyawun asali da tushe a ko ina an san kasar Hausa....." Kadan kenan daga cikin Baitocin wakar Mai Asayyaro da yake  nuni da kuma tabbatar da irin tsari mai kyau na al'adun rayuwar Kasar Hausa wanda tun asali aka san Mallam Bahaushe dasu. Tabbas haka yake musamman in mukai duba da irin yadda al,ummomi cikin fadin duniya ke nuna hakilonsu da sha'awarsu dangane da al'adun kasar Hausa.
Biki, bidiri, burede shine kirarin da akewa Bikin aure wanda na daya daga cikin abubuwa masu matukar mihimmanci a al'adar hausawa, akan sanya ranar bikin aure na tsawon lokaci don samun damar  shiryawa tsaf don tunkarar bikin. Akan tanadi abubuwa daban daban da suka hada da kayan abinci, tufafi na ado da kawa  da sauran abubuwa na al'ada domin kece raini da fita kunya.
A bikin aure iyayen amarya sunfi maida da hankali kasancewar su zasu wanke su bayar, shi yasa shagulgulan bikin suka fi yawa a gidan amare,  a al'adance yayin da bangaren amarya suke gudanar da kamun amarya, sa lalle, wunin biki, kafi ko danki, wankan amarya, rakiyar amarya, budar kai har zuwa ranar da baki zasu watse, su ma dangin angon a nasu bangaren ba a barsu a baya ba domin akwai shagulgula da suka hada da kamun ango, daurin aure, zaman ajo, chuda, sayen baki da kuma tasani. Haka kuma saboda kawaici, kamun kai da kuma kunyar mallam bahaushe, dukkan wadannan sabgogin bikin na al'ada ba inda ake cudanya maza da mata sai wajen sayen baki inda abokan ango da kawayen amarye ke yin rakiya. Wadannan abubuwan su aka fi sani a kasar hausa wajen gabatar da bikin aure, kodayake a wasu lokutan al'adun sukan sha bamban daga gari zuwa gari a fadin kasar hausa amma akasari akwai kamanceceniya a bikin kanawa, katsinawa, hadejawa, zazzagawa, sakkwatawa da dai sauran garuruwan hausawa.
Sai dai kash! Abin takaicin a halin yanzu an gurbata bikin aure a kasar Hausa ta hanyar aron al'adu wadanda basu da kyau kuma basu dace da hausawa ba kwata kwata, aka gwamasu da na hausawa, a wasu lokutan ma da yawa akan watsar da zubi da tsarin bukin aure na al'ada a dauko na zamani wanda ke cike da rashin kunya da zubar da kima a tsakanin surukai, dangi da kuma maauratan. Abinda yasa nace haka shine, a halin yanzu dabi'ar turawan yamma ta mamaye bukukuwa a kasar hausa ta inda tun a farko kafin akai ga daura aure a lokuta da dama wasu angwaye da amare kan dauki hotuna na rashin kunya da takaici da sunan yin amfani dasu a abubuwan da za'a raba kyauta a wajen biki (souvenir), sai kaga a tsakiyar kasuwa ana yawo da jaka ko wani abu dauke da hoton amarya da ango, 'ya'yan hausawa cikin fita ko shiga mara mutunchi da kamala, wadannan hotunan suna ciwa jama'a kishin addini tuwo a kwarya don kuwa abun na neman zama al'ada. Yanzu kam hatta kamun amarya zamani ya gurbata shi, akan gudanar dashi a gwamatse maza da mata, iyaye, yan uwa, abokai da kawayen ango da amarya, ana kida ana rawa har ta kai ga uwar amarya zata iya fitowa ta taka rawa a gaban surukinta da abokansa harma su yi mata likin kudi, haka suma ango da amarya za'a basu fagge don su taka rawa a gaban surukansu. Tab! Allah wadaran naka ya lalace. Abinda na sani na al'ada dangane da kamun amarya shine amarya kan gudu wani wurin da ba'a sani ba, akan kuma sha wahala wajen nemanta gida-gida kafin a gano inda take don a kamata, amma yanzu kam a bayyane amarya ke zuwa da kafarta wajen da aka tanada don yin kamu cikin taron maza da mata har wani lokacin ma a yanka Kek, ango ya sawa amarya a bakinta ita ta yanko ta sanya masa a baki wai duk a wajen kamu, Tirkashi! Me yakawo dabi'ar Yahudu wan Nasara kasar Hausa? Nasan a iya cewa zuwan turawan mulkin mallaka ne ya kawo irin wannan badakalar musamman yadda suka nuna fifikon al'aldunsu fiye da namu kuma wai wasunmu suka aminta da hakan madadin muyi riko da namu mu kuma nuna musu mun fisu tinkaho da alfahari  da al'adunmu na kasar hausa.
Yanzu har akwai shagulgulan da akewa laqabi da (european night, indian night  Arabian night da sauransu) inda ake raqashewa da holewa dai dai da tarbiyar jinsin  mutanen da aka ambata a wannan daren. Duk da yake wasu al'adun bahaushe basu dace da addini ba amma tambaya ta anan itace shin da mu da turawan yamma su waye al'adunsu suka fi cin karo da addinin musulunci?
Akwai bukatar duba izuwa addini da al'adu masu kyau wajen tafiyar da rayuwarmu musamman wajen gudanar da bukukuwan aure don kada mu rika aiwatar da abubuwan daAllah zai fushi da shi tun a lokacin gudanar da shagulgulansa.
Iyaye nada mihimmiyar gudummawa wajen gujewa irin wannan tabargazar da ake aikatawa da sunan wayewar zamani. Na tabbata irin sabgogin bikin hausawa wadanda na ambata a baya suna da matukar tasiri wajen kiyaye mutuncin ma'aurata a tsakanin dangi da abokan arziki, kuma addinin musulunci wanda hausawa suka karba yayi hani da cudanya tsakanin maza da mata don gudun afkuwar wata badalar, saboda haka tilas ne mu guji dukkan abinda zai kawo debewar albarkar aure.
Allah yasa muji mu kuma yi watsi da dukkan al'adun banza musamman irin wadanda yahudawa da turawan yamma suke kokarin cusa mana.
MUDASSIR ya rubuto daga NTA Zariya.

No comments:

Post a Comment