Friday 19 September 2014

YUNKURIN KOYI DA HALAYEN SARDAUNA;
BA GIRIN GIRIN BA…….

DAGA
MUDASSIR ALIYU YUNUSA

     Masu Magana na cewa “Wawaye adon tafiya”, wannan haka yake bisa la’akari da tafiyar da ake aiwatarwa a yankin arewacin Najeriya wadda take bukatar waiwaye domin kawata tafiyar a halin yanzu, tun bayan rasuwar Mai girma Firimiyan tsohuwar jihar arewa Alhaji Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato (Gamji dan kwarai, Namiji uban yan boko) ake samun ja baya a arewacin kasannan duk cewar an samu karuwa ta fuskoki da dama da suka hada da yawan masu ilimi, wayewa, arziki sannan kuma an sami saukin aiwatar da wasu abubuwa ba kamar lokacin da ba, amma sai dai babu ci gaba ta fuskar tattalin arziki, siyasa da kuma jin dadi da walwalar jama’a musamman ga talakawan yankin. Abin tambaya anan shine me ya jawo wannan koma bayan? Lallai idan muka waiwayi irin halaye da dabi’un Marigayi Firimiyan zamu tabbatar da bukatar koyi da su a wannan lokaci da yake cike da sammatsi ta fuskar jagoranci, zamantakewa tattalin arziki da siyasa. Yana da kyau kwarai mu tuna irin abubuwan cigaba da yankin arewa ya samu a lokacin Firimiya wadanda har a yau muna cin moriyar wasunsu da suke nan kuma muke takaicin rashin wadanda suka durkushe daga cikinsu. Bama yan arewa kadai ba wasu ma a yanzu dasu kasar take takama.
      Misali, a bangaren ilimi koda yake dama akwai ilimin addini, karatu da rubutu tun kafin zuwan turawa amma ta fuskar ilimin boko kowa ya san irin babban aikin da Gamji ya yiwa yankin arewa, an sami cigaba ta hanyar gina makarantun ilimin zamani tun daga kan elemantiri, sakandire har zuwa kan manyan makarantun gaba da sakandire kamar makarantar nazarin kimiyya, fasaha da harkokin yau da kullum ta Kaduna (Kaduna Polytechnic)  kai har ma da jami’o’i  irin su jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria (ABU) a yankin na arewa. Wannan ya ba arewacin Najeriya damar yin gogayya da sauran sassan kasar duk da sun yi mana nisa ta fuskar ilimin zamani.
     Ta fuskar tattalin arziki kuwa, kowa yasan arewa akan Noma, Kiwo da sauran sana’o’in hannu irin su saka, kira, rini, dinki, jima, dukanci, sassaka da sauransu, wadannan sana’o’in sun sami kula sosai a lokacin Firimiya inda ya jajirce wajen zamanantar dasu domin su yi daidai da wancan lokacin. An sami damar kafa Masaku a Kaduna, Funtua da Gusau; Masana’antar sarrafa gyada; kamfanin Madara na Arewa wandanda suka taimaka matuka wajen samar da ayyakan yi ga jama’ar arewa suka kuma bunkasa tattalin arziki da daukaka darajar yankin arewa.
     A bangaren cinikayya da kasuwanci Sardauna ne ya samar da tsohon Bankin Arewa (Bank of the North) da Kamfanin cigaban Nijeriya ta Arewa (Northern Nigerian Developmen Company) domin bunkasa harkokin kasuwanci wanda sun kai makura wajen taimakawa al’ummar da tallafi don habaka kasuwanci, noma, muhalli da cigaban jama’ar yankin. Dadin dadawa idan mu kayi duba zuwa bangaren wayar da kan al’umma da ilimantarwa baza mu manta gidan rediyon ta talabijin na Kaduna dana kano da sauran kafafen watsa labarai a yankin wanda suke karkashin kulawar (Broadcasting Comapany of Northern Nigeria) da kamfanin dab’i na arewa ba (Northern Nigerian Publishin Company), da kamfanin jaridu irin su “New Nigerian” da Gaskiya tafi Kobo wandanda suka taimaka matuka wajen wayarwa da ilimantar da jama’a ta fuskar addini, zamantakewa, siyasa, kiwon lafiya, tattalin arziki da sauransu.
     Hakikanin gaskiya idan muka yi duba izuwa ayyukan cigaba da Sardauna ya kawo arewa zamu tabbatar ya zarta sauran takwarorinsa Firimiyoyin yankunan gabas da yamma na kasarnan, Sir Ahmadu Bello ya zamo zakaran gwajin dafi a tsakanin su ta fuskar samar da jin dadi da walwalar jama’a duk da cewar yankin da yake jagoranta yafi sauran yankunan girman kasa, yawan jama’a, bambancin addini, kabilu, al’adu da dabi’u amma duk da haka yankin ya samu cigaba fiye da sauran a wancan lokacin, tabbas wannan ya samo asali ne bisa jajircewarsa bisa aldalci da kuma sanin hakkin talakawansa.
     A halin yanzu abubuwa da dama sun tabarbare a arewa inda yankin ke fuskantar babbar barazanar durkushewar martabar da magabatan suka dora yankin akai. Ada jama’ar arewa suna cike da walwala, jindadi da kwanciyar hankali, amma yanzu labarin ya sha bamban bisa la’akari da halin kunci, masifar talauci wanda alkalumma suka nuna karfinsa fiye da a sauran yankunan kasarnan. Haka kuma bincike ya nuna an fi samun yawan cututtuka da ballewar annoba a arewa, sannan kuma yankin yafi ko ina a fadin kasarnan yawan yara kanana marasa zuwa makaranta da suka dogara da aikatau a gidajen masu hannu da shuni, yan siyasa da manyan jami’an gwamnati, wannan ya samo asali ne ga irin sakaci, halin ko in kula da kuma rikon sakainar kashi da jagororin arewa na wannan lokacin ke wa jama’arsu sabanin yadda Marigayi Sardauna ya tafiyar da shugabancin ga mutanen arewa.
     Yau shekaru 48 da durkushewar gwamnatin yankin arewa, an kuma kasafta yakin zuwa jihohi 19 wandanda gwamnoni 19 ke gudanar da sha’anin mulkinsu ba tare da la’akari da juna ba. To abin lura anan shine yadda jagora daya tilo ya jagoranci daukacin jama’ar yankin kuma aka samu cigaba mai amfani ga jama’a, ina ganin zai zamo da sauki a yanzu a wajen mutane 19 (Gwamnoni Jihohin Arewa). Alhamdulillah, a iya cewa su kansu jagororin suna yabawa da irin salo da jagorancin Firimiya don kuwa sukan bada misali su da kansu, kaga kenan a iya cewa ko sun gano bakin zaren ne sun kuma yi amanna da cewar akwai matsaloli a yankin kuma dawo da martabar arewa bai yiyuwa sai anyi adalci kamar yadda Sardauna yayi ada, sai dai mutane suna ganin ba’a nan gizo yake sakar ba, babbar maganar itace yadda za’ayi amfani arzikin yankin wajen dawo da martabar arewa ta fuskar yaki da talauci, bunkasa lafiya, inganta ilimi, bunkasa aikin noma, farfado da masana’antu, cigaban ciniki da kasuwanci da kuma kyautata siyasa da harkokin mulki da kuma uwa uba tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.
     Lallai in har za’ayi kokarin aiwatar da abubuwan da aka gabatar a lokacin gwamnatin Firimiya Sa Ahmadu Bello to ba makawa talakawan arewa zasu dara, yan kasuwa zasu sami cigaba sannan kuma shugabannin arewa zasu sami nutsuwa gami da san barka daga wajen wadanda suke jagoranta. Haka kuma arewa zata zamo abar misali, abar alfahari kuma abar kwaikwayo ba ma kadai ga sauran yankunan kasarnan ba har ma ga sauran kasashen duniya masu kishin talakawansu baki daya.
     To amma fa hakan baza ta samu ba sai an sami mutane na gari masu adalci, rikon amana, gaskiya, tausayi, juriya, hakuri da kuma uwa- uba tsoron Allah. Sannan mu kuma jama’a mu basu hadin kai da goyon baya mu kuma kyautata musu zato kuma muyi musu addu’a domin samun nasara ga wannan muhimmin kudirin da ni, kai, ke zamu amfana da kuma yayanmu da jikokinmu su mora a nan gaba.

MUDASSIR ya rubuto daga NTA Maiduguri.





No comments:

Post a Comment